Tattalin arziƙin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na 2024 – NBS

0
15
Tattalin arziƙin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na 2024 - NBS

Tattalin arziƙin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na 2024 – NBS

Tattalin arziƙin Najeriya ya ƙaru da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na shekarar 2024.

A cewar rahoton bunƙasar tattalin arziƙin da hukumar ƙididdigar Najeriya (NBS) ta fitar a yau Talata, bunƙasar ta dara kaso 3.46 da aka samu a zango na 3 na 2024.

KU KUMA KARANTA:Za mu faɗaɗa mizanin tattalin arziƙin Najeriya da ɓoyayun sassan da ke samar da kuɗi – NBS

Alkaluman na yau Talata game da zango na 4 na shekarar 2024 sun kuma dara kaso 3.46 cikin 100 da aka bada rahoton samu a zagon na 4 na 2023.

Bangaren ayyuka ne ya mamaye galibin bunkasar ta zango na 4 na 2024, wanda ya karu da kaso 5.37 cikin 100 tare da bada gudunmowar kaso 57.38 cikin 100 na jumlar tattalin arzikin,” a cewar wani bangare na rahoton na NBS.

Leave a Reply