Tankokin yaƙin Isra’ila sun shiga kudancin birnin Rafah na Gaza — Rahoto

0
90

Tankokin yakin Isra’ila sun shiga birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza, inda suka kai kusan mita 200 daga tsallaken Masar, kamar yadda wani jami’in tsaron Falasɗinu da wani jami’in Masar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP.

Jami’in na Masar ya ce da alama “aikin” yana da iyaka. Shi da tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Hamas sun ce jami’an Isra’ila sun sanar da Misirawan cewa dakarunsu za su janye bayan kammala aikin.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ce ta aika da kayan agaji  mafi yawa zuwa Gaza da ya kai tan 50,000 — Erdogan

Jami’in na Masar da ke yankin Rafah na ƙasar Masar da kuma jami’in tsaron Falasɗinawa sun yi magana ne da manema labarai.

Tun da farko a ranar Litinin, Majalisar Ministocin Yakin Isra’ila ta yanke shawarar ci gaba da kai farmakin soji a Rafah, bayan da kungiyar Hamas ta sanar da amincewa da shawarar Masar da Qatar na cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Leave a Reply