Tallafin wutar lantarki ya ƙaru da kaso 2.76 cikin 100 – NERC
Yawan kuɗaɗen tallafin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke zubawa wajen samar da lantarki ya ƙaru zuwa Naira biliyan 199.64 a watan Disamban 2024, a cewar bayanan da aka samo daga hukumar kayyade farashin lantarki ta Najeriya (NERC).
A cewar rahoton da aka fitar tallafin wutar lantarkin ya ƙaru da kaso 2.76 cikin 100 zuwa Naira biliyan 199.64 a watan Disamban da muke ciki daga Naira biliyan 194.26 da ya kai a watan Nuwamban da ya gabata.
NERC ta ƙara da cewa, ƙarin da aka samu a harkar musayar kuɗaɗe da ta ƙayyade farashin dala a kan Naira 1, 687.45 da karuwar hauhawar farashi zuwa kaso 33.9 cikin 100, da kuma sauye-sauyen da aka samu wajen samar da lantarkin ne suka sabbaba samun dan karin.
Rahoton ya nuna cewa gwamnatin tarayyar ta bar farashin lantarkin a yadda yake ga dukkanin rukunonin masu amfani da wutar.
KU KUMA KARANTA: Kasafin kuɗin da na gabatar wa Majalisar Dokoki na farfaɗo da ƙasan ne – Shugaba Tinubu
A yayin da rukunin kwastomomin dake kan damarar “A” suka ci gaba da biyan Naira 209 a kan kowane kilowat na lantarkin, an amince farashin da kwastomomin dake kan damarar “E” za su biya ya tsaya a yadda yake a watan Disamban 2022.