Ta’aziyyar Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) a ranar arba’in
Daga Ibrahim Sheme
- Al-Mujibu ka ba ni tanyo,Zantuka domin in shiryo,Ba gwaninta ai a koyo,Addu’a ce za ni ɗan yo,Ta rashin ‘yar’uwar mu Daso.
- Gaisuwa ta ta taƙaita,Gun mafificin halitta,Ɗaha mai zurfin fahimta,Ɗan Amina uba ga Binta,Wanda tai ƙaunar sa Daso.
- Mutuwa mai wafce kaɗo,‘Yar Fulani ce ta fyaɗo,Saratun mu ɗiyar Giɗaɗo,Ba sanarwa ta saɗaɗo,Ta yi wuf da ƙawar mu Daso.
- Saratun mu ɗiyar Muhamman,‘Yar Kano ce ita wannan,Jaruma a Kannywood sannan,Ayyukan ta a duniyar nan,Sun yi tasiri da naso.
- Tun da farko rayuwar ta,Ta yi ticin makaranta,‘Yan firamare fa mata,Har mazan duk ta ƙagauta,Gun batun koyon su, Daso.
- Sai ta tsoma ƙafa a harkar Shirya fim ku ji don ku sadar,Kamfanin su Sarauniya har,Masu barci duk ta farkar,Masu so har wanda bai so.
- Tai fice a finafinan mu,Mun gani a akwatunan mu,Can ta hasko rayuwar mu,Dariya ta saka a ran mu,In tana aktin ta Daso.
- Masu fim kaf ba kamar ta,In mugunta suka sa ta,Kishiya ko ko uwar ta,Za ta yi shi iya gwaninta,Yadda daraktan ta ke so.
- Shi fa rol in dai ta taka,In na kirki babu shakka,Ko na assha ne ta tafka,Sai a ce, “Allah ya saka,Ya biya burin ki Daso.”
- Ban da fim ɗin, kar ku manta,Gun ciyarwa kun fa san ta,Tallafin duk mai buƙata,Yara, tsofaffi da mata,Ko a nan lada ta kwaso.
- Tai rabo na ruwa, abinci,Masu so a gare ta sun ci,Ga tufafi – har ga zuci –Ta kira mai shara barci:“In kana so, to ka taso.”
- Ran da Ramadan ya ƙare,Malamai suka ce a daure,Ai talatin kar a sare,Shi ta ɗauka don ta more,Don cikar ladar ta Daso.
- Tai shirin Sallah da maiƙo,To ashe da akwai fa saƙo,Ba daɗewa ta yi baƙo,Ran ta ne aka ce ya miƙo,Ya taho, haka Hayyu ke so.
- Tai sahur, sallah, ta kwanta,Sai ta ce, “Bari dai na huta,”Rabbana ya katse zaman ta,Can da hantsi ‘yar’uwar ta,Tai kira, ai ba ta taso.
- Duk gari kowa ya ruɗe,Zuciyoyi suka bauɗe,Lamarin jama’a ya cuɗe,Duk kalar kowa ta koɗe,Ko zuma ma ba ta laso.
- Duk masoya sun saduda,Dandazon jama’a mashaida,Sun yi sallar ta a Fada,Daga nan tafiya ta idaGun kushewa tata Daso.
- An rufe ta ana ta kuka,Turbuɗe ta akai a laka,Zuciyoyi na ta duka,Sai du’a’i ke ta sauka:“Al-Gaffar yafe wa Daso!”
- Na yi kuka har a ƙalbi,Na siƙe a wajen jawabi,Nai diƙin a wannan babi,Ba ni don in wanke gurbi:Sabulu da ruwa da soso.
- Addu’ar mu tutur gare ta:Zuljalalu ka jiƙan ta,Baɗinin ta da zahirin ta,Yafe dukkan kurakuran ta,Sa ta Aljannar ka, Daso.
- Muna ta roƙo gun Ta’ala:Yafe laifukkan ta Jallah,Kuskuren da ita ta ƙulla,Don cikar azumi da sallah,Ba ta duk rahamar ka, Daso.
- Arba’in yau tun rashin ta,Mun yi jimami a kan ta,Gaisuwar mu ga ‘yan’uwan ta,Har da ‘yan Kannywood zumun ta,Don rashin sistar su, Daso.
- Malamai ai sun ishara:Yadda Maiduka duk ya tsara,Ba tsimi kuma ba dabara,Ƙaddara ce babu gyara,Sai abin da Ƙahharu ke so.
- Mu da ke nan ba mu kuri,Duk daɗewa ko ko sauri,Ko da rama ko da kauri,Ko da zaƙi ko da bauri,Za mu je mu ishe ta Daso.
- Wagga waƙar ba bajinta,Iro ɗan Mamman ya yi ta,Sheme mai Binta da Binta,Har ku sa Auta ta Mata,Addu’a ce don ta Daso.
- Baituka ashirin na jera,Sai biyar a sama na ƙara,Don cikar roƙon Tabara,Na yi roƙon ba gadara,Don biɗar rahama ga Daso.
Alhamdu lillahi!