Ta sha guba ta mutu, saboda mijinta ya yi wa wata budurwa ciki

Wata mata mai matsakaicin shekaru mai suna Misis Bose Odunayo, ta kashe kanta a jihar Ondo, saboda mijinta ya yi wa budurwarsa ciki.

Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne a unguwar Igoba da ke Akure, babban birnin jihar Ondo.

A cewar jaridar mallakin gwamnatin jihar, an ruwaito cewa mahaifiyar ‘ya’ya huɗu ta sha maganin ƙwari ne bayan da ta samu ƙiran barazana daga ɗaya daga cikin dadiron mijinta da ta yi iƙirarin cewa tana ɗauke da cikinsa.

An samu labarin cewa an kwashi ‘yan kallo lokacin da iyalan mamacin suka zo da gawarta kwatsam daga garin Akoko domin yi mata jana’iza a gidan mijinta da ke Akure, inda ake gudanar da addu’oi kafin a binne gawar.

KU KUMA KARANTA: Wata matashiya a jihar Abiya, ta kashe mahaifiyarta ta hanyar sa mata guba a abinci

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa marigayiyar wadda ta sha guba a gidanta da ke unguwar Igoba a Akure, nan take ta nufi garinsu da ke Ifira Akoko, domin sanar da iyayenta cewa mijin nata zai yi sanadin mutuwarta ba tare da wani ɓata lokaci ba sakamakon hulɗarsa da ‘yar dadiro.

A cewar wata majiya daga dangin, kafin marigayiyar ta mutu, ta ce dadiron mijinta ta zarge ta da laifin zubar da cikin da ta samu.

Mijin wanda mamba ne na ƙungiyar ma’aikatan sufuri ta ƙasa, NURTW, a Akure, ya ce marigayiyar matarsa ​​ta ɗauki kayan ta tafi garin iyayenta da ke Akoko, sai kawai ya ji labarin rasuwar ta.

“Matata ta yi iƙirarin cewa ita ce ke kula da duk wasu kuɗaɗe a gidan da suka haɗa da biyan kuɗin makarantar yara wanda a zahiri ba gaskiya ba ne,” in ji shi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *