Ta roƙi kotu ta raba aurensu, saboda rashin kulawa daga mijinta

0
303

Wata ‘yar kasuwa, Anthonia Ubong, a ranar Litinin, ta roƙi wata kotun al’ada da ke zamanta a Jikwoyi, Abuja, da ta yi wa mijinta addu’ar rabuwar aure bisa dalilin rikicin cikin gida.

Anthonia ta gabatar da buƙatar ne a ƙoƙarinta na ƙare ƙarar da mijinta, Mista Ime ya shigar.

Ta ce, “Mijina ba ya ba ni abinci. Ya murguɗa kafata a lokacin da na ce ya ba ni Naira 100 in saya abinci a lokacin ina da ciki wata takwas.

KU KUMA KARANTA: Ta nemi a raba aurenta, saboda rashin soyayya da kulawar mijinta

Ciwon ƙafa na bai daina ba sai da na haihu. “Ya kuma ƙi biyan Naira 60,000 na tiyatar da na yi na haifi jariri bayan na yi naƙuda mai tsawo.

Mama da ƙanwata ne suka biya kuɗi suka kula dani. Naira 4,000 kawai mijina ya ba ni.”

Ta kuma yi zargin cewa mijin nata ya yi mata naushi a fuska tare da raba ƙashinta, inda ta ƙara da cewa ya girme ta da shekara 11 don haka bai yarda ta ce komai ba a auren.

Ta roƙi kotu da ta raba auren ta kuma ba ta riƙon ‘ya ɗaya tilo da ta haifa. Mai shari’a, Misis Thelma Baba, ta ɗage sauraron ƙarar, zuwa ranar 28 ga watan Satumba, domin yi mata tambayoyi.

Leave a Reply