Ta rasu bayan an yi mata tiyata a tuwon ɗuwawu

0
341

Wata budurwa ‘yar shekara 23 mai suna Destiny Benjamin, ta mutu kwanaki huɗu bayan da aka yi mata tiyata a tuwon ɗuwawunta (hips), wadda aka fi sani a turance da Brazilian Butt Lift, BBL, a Cynosure Aesthetic Plastic Surgery, a Legas.

Shafukan sada zumunta daban-daban sun yi ta yawo da faifayin bidiyon yadda aka yi tun bayan rasuwarta. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai kamfanin Cynosure Aesthetic Plastic Surgery, Dakta Ogbe Omoruyi, ya musanta zargin da ake na cewa matar ta rasu ne a Asibiti lokacin da ake yi mata tiyata ɗin.

KU KUMA KARANTA: Dattijuwa mai shekaru 83 ta mutu bayan ta ci kifi yayin da ake ƙoƙarin ceton ran mijinta

Omoruyi, wacce ta zanta da jaridar Vanguard, ta bayyana cewa, an yiwa marigayiyar tiyatar ne a ranar 8 ga watan Maris, kuma ta koka da wahalar numfashi kafin a kai ta Asibitin Ƙwararru na Genesis dake Ikeja, a birnin Legas, inda ta mutu.

Omoruyi, wanda kuma Likitan fiɗa ne, ya ƙara shaida wa jridar Vanguard cewa marigayiyar tana da shekaru 23 a duniya ba 20 ba. Ya ce: “Yarinya ce ‘yar shekara 23 bisa ga abin da ta rubuta a kan takardunta.

An yi mata tiyata bayan ta samu lafiya, tiyatar ta yi kyau. “Zan iya nuna muku a cikin bayanin shari’ar mu don nuna cewa komai ya yi kyau. “Duk da haka, bayan kwanaki tana fama da wahalar numfashi.

Mun sanya ta a kan iskar ‘oxygen’ kuma ta samu sauƙi kafin mu tura ta zuwa sashin kulawa mai zurfi, wanda ke da nisan mintuna 10 daga wurin mu.

“An gudanar da bincike mai matukar muhimmanci. Ana kiransa ‘CT Pulmonary Angiogram’. Wannan zai iya gano kowane gudan jini da ke cikin tsarin huhu. “An yi gwajin ne a wurin da aka tura ta.

Lokacin da aka sanar da ni kuma na nuna sakamakon, an ce ba ta da ciwon ciki. “ɗan uwanta, Sunset, yana tare da ita bayan tiyatar da aka yi mata. Sun zagaya don suna tare. Tana zuwa ya ganta sannan suka ɗauki hotuna tare, suna zagaya a harabar Asibitin bayan kwana biyu.

“Wannan shi ne don na sanar da ku cewa tana cikin koshin lafiya bayan tiyatar. “Duk da haka kuma abin takaici, ba a yi gwajin gawarwaki ba; Ban sani ba ko iyali za su yarda da a yi hakan.

“Saɓanin rahotannin kafofin sada zumunta na yanar gizo da ke cewa Asibitin kiwon lafiya ya yi rahoton mutuwar mutane biyar a cikin shekara guda, Ogbe ya ce an samu mutuwar mutane biyu ne kawai a Asibitin, inda ya ce lamarin ya faru ne a shekarar 2018 da 2021.

Ya ce: “Za a iya tabbatar da hakan ta ƙaramar hukuma, domin dukkan ƙananan hukumomin suna da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko, inda ƙwararru ke ba da rahoton adadin waɗanda suka mutu.

“Don haka, muna da mutuwar mutane biyu kawai.”
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce: “A iyakar sanina, ban san da faruwar lamarin ba. “Iyalan mamacin ba su kawo rahoto ga hukumar ‘yan sanda ba.”

Ƙoƙarin samun bayani daga Asibitin Ƙwararru na Genesus ya ci tura. Sai dai wanda ya amsa kiran jaridar Vanguard a lokacin da aka buga labarin ya ce bai san abin da ya faru ba.

Leave a Reply