Ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da yaƙi kan yin hijira ba bisa ƙa’ida ba

Firayim Minista na hannun dama na Italiya Georgia Meloni ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya da ta ƙaddamar da “yaƙin duniya” kan hijira ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan na zuwa ne a yayin da kwale-kwalen baƙin haure suka sake sauƙa a tsibirin Lampedusa da ke gaɓar tekun Bahar Rum na Italiya.

Da take magana a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York, ta yi ƙira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta ƙaddamar da “yaƙin duniya” kan masu safarar mutane.

A ranar alhamis, sama da mutane 700 ne suka isa tsibirin cikin sa’o’i a cikin kwale-kwale daga Afirka, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ruwaito.

Tun daga ranar Laraba, sama da sabbin jiragen ruwa 20 ne suka sauƙa, yawancinsu daga ƙasar Tunisiya.

KU KUMA KARANTA: Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da sakin yara 21 da aka yi garkuwa da su

Cibiyar karɓar baƙin haure ta Lampedusa ta kasance cike da cunkoson mutane sama da 1,100.

Ƙaramin tsibiri na Lampedusa, dake tsakanin Sicily da Arewacin Afirka, ya kasance wurin yin hijira na Turai tsawon shekaru.

A makon da ya gabata, dubban baƙin haure sun sake sauƙa a can cikin kwale-kwale daga Arewacin Afirka, inda sama da 5,000 suka isa a rana guda.

Hukumomin can sun kafa dokar ta ɓaci. A ƙarshen mako, Meloni ya ziyarci tsibirin tare da shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

A yayin jawabinta na Majalisar Ɗinkin Duniya, Meloni ta ce: “Na gamsu da cewa aikin wannan ƙungiya ne ya shelanta yaƙin duniya kan masu safarar mutane ba tare da munafunci ba kuma ba tare da tsangwama ba.”

Italiya, in ji ta, a shirye ta ke ta kasance kan gaba a wannan. Meloni tana jagorantar gamayyar jam’iyun dama na kusan shekara guda.

Magance hijira ba bisa ƙa’ida ba na ɗaya daga cikin muhimman alƙawurran zaɓe da ta yi.

A cewar ma’aikatar harkokin cikin gida, baƙin haure 130,000 ne suka isa Italiya ta teku tun farkon shekarar l, wanda ya ninka kusan sau biyu a daidai wannan lokacin a shekarar 2022.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *