Rundunar haɗin gwiwa mai yaƙi da sharar gida a birnin Kano ta ce ta kwashe sama da Tireloli 400 na sharar gida a cikin kwanaki uku da gudanar da aikinta.
Babban Sakatare na Ma’aikatar Muhalli, Aliyu Garo, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin wani bincike da sa ido kan kwashe shara a birnin ranar Juma’a.
Garo ya ce Gwamna Abba Yusuf ya kafa wata rundunar haɗin gwiwa don gudanar da aikin kwashe sharar a cikin birnin Kano.
KU KUMA KARANTA: Ganduje ya sayar da dukkan motocin kwashe shara na gwamnatin Kano – Gwamna Abba
Ya ce kwamitin na ƙarƙashin jagorancin Haruna Ɗanzago ne a matsayin Sakatare. Ya ce manufar rundunar ita ce tabbatar da zubar da shara yadda ya kamata a manyan titunan Kano domin tsaftace shi.
“Haka kuma don kaucewa toshe hanyoyin ruwa da kuma hana ambaliya, musamman a lokacin damina,” in ji Garo.
Ya buƙaci mazauna garin da su saba da al’adar share magudanan ruwansu akai-akai don gujewa ambaliya. Ya yaba da jajircewar siyasar da gwamnan ya nuna wajen kare rayukan mutane ta hanyar inganta tsaftar muhalli.
Garo ya kuma yaba masa bisa ɓullo da wasu sabbin abubuwa da suka haɗa da tilasta yin amfani da kwanduna da masu ababen hawa ke yi.
Don haka, Garo, ya buƙaci mazauna yankin da su ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin gwamnati na ceto muhalli daga haɗurran sauyin yanayi.
Da yake jawabi a madadin al’ummar yankin Kurna Asabe da ke ƙaramar hukumar Dala, wani shugaban al’ummar yankin, Usman Nuhu, ya gode wa gwamnan bisa ɓullo da shirin tsaftace muhalli, inda ya bayyana hakan a matsayin wanda ya dace.
Ya ce sharar da aka tara a cikin babban birni na da matuƙar haɗari ga lafiyar mazauna yankin.
[…] KU KUMA KARANTA: Ta kwashe tan 400 na sharar gida daga cikin birnin Kano – Hukuma […]
[…] KU KUMA KARANTA: Ta kwashe tan 400 na sharar gida daga cikin birnin Kano – Hukuma […]