No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wani ɗan kasuwa mai shekaru 40 ya shiga hannun hukuma bayan an kama shi dumu-dumu yana lalata da ’yarsa mai shekara biyar da yayarta mai shekaru bakwai.

Wata kotun majistare da ke Ikeja babban birnin jihar Legas, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare magidancin a gidan yarin a Kirikiri bisa zargin lalata da ’ya’yansa mata biyu.

Mai Shari’a, Misis Bola Osunsanmi, ta ƙi sauraron wanda ake ƙara, ta ɗage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Yuni.

Ta ce za ta saurari shawara daga Daraktan shigar da ƙara na kasa kafin wannan lokacin.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa tun da farko, ɗan sanda mai gabatar da kara, ASP Raji Akeem, ya shaida wa kotun cewa a watan Satumba na 2021, matar wanda ake ƙara ta kama shi yana lalata da ’yarsu mai shekara bakwai.

KU KUMA KARANTA: An kama wata malama da laifin yin lalata da ɗalibanta

Yayin da a watan Mayu, 2024, matar ta ƙara kama shi yana ƙoƙarin lalata da wata ’yar tasu mai shekaru biyar.

Abin da ya fusata ta, ta kai ƙararsa ga hukuma.

Mai gabatar da ƙarar ya ce, waɗannan laifuka sun saba wa sashe na 137 na dokar laifuka ta jihar Legas da aka inganta a 2015.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...