Ta damƙe mazakutar mijinta, ya mutu har lahira

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke wata mata bisa mutuwar mijinta, Jakpo Ekemini, a unguwar Mosogar da ke ƙaramar hukumar Ethiope ta Yamma a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Bright Edafe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Warri a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, 2023, ya ce matar ta ja mazakutar mijin nata mai shekaru 32 a duniya a lokacin wata rigima a tsakaninsu.

“Ba ta yanke mazakutar ba, sai dai ta damƙe su da ƙarfi ta ja su,” in ji PPRO.

“Mutumin ya mutu sakamakon wannan lamari,” in ji shi.

Wata majiya da ta san lamarin, ta shaida wa manema labarai cewa, babban yayan marigayin ne ya kai rahoton lamarin a ranar Talata ga ‘yan sandan yankin da ke Mosogar.

KU KUMA KARANTA: Ta nemi a raba aurenta, saboda rashin soyayya da kulawar mijinta

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata 12 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 1:20 na rana sakamakon rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin ma’auratan.

“Matar ƙanina (an sakaya sunanta) ta damƙe kuma ta ja mazakutar mijinta, Efemini, mai shekara 32 a lokacin da suke faɗa a Mosogar.  Ana cikin haka sai ƙanina ya faɗi aka garzaya da shi asibiti inda daga baya aka tabbatar da cewa ya rasu. An ajiye gawar a ɗakin ajiyar gawarwaki da ke Mosogar,” majiyar ta ruwaito ɗan uwan ​​marigayin yana cewa.

An tattaro cewa wanda ake zargin ta gudu zuwa inda ba a sani ba bayan ta aikata laifin. Daga baya an kama ta kuma a halin yanzu ana yi mata tambayoyi a hannun ‘yan sanda.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *