Suna Muhammad ya sake zama kan gaba a sunayen da ake raɗawa jarirai a ƙasar Ingila
Daga Jameel Lawan Yakasai
An fitar da sunayen jarirai da suka fi tashe a shekarar 2024 a Ingila da Wales, inda Athena da Yahya suka shiga cikin guda 100 na farko da aka fi sanya wa yara a karon farko.
A Muhammad ya zama na ɗaya a ɓangaren maza, shekara biyu ke nan a jere, inda Noah da Oliver suka zo na biyu da na uku, kamar yadda yake a shekara ta 2023.
Olivia da Amelia ne sunayen yara mata na ɗaya da na biyu da aka fi sanyawa, karo na uku a jere, sai dai Isla ya fita daga cikin ukun farko a sunayen da aka fi sanya wa yara mata, inda Lily ya maye gurbinsa.
KU KUMA KARANTA: Mace ta farko da ta musulunta a Liverpool, Ingila
Ofishin ƙididdiga na Birtaniya ne ya fitar da alƙalumar, wanda shi ne ke tattara bayanan takardar rajistar haihuwa.
Sabbin sunayen yara mata da suka shiga 100 na farko su ne Eloise da Nora da Myla da Rosa da Athena da Sara da kuma Zoe.
A ɓangaren maza kuma akwai Austin da Nathan da Vinnie da kuma Yahya.
Muhammad ya kare kambinsa na sunan da aka sanya wa jarirai maza ne inda aka sanya wa yara 5,721 sunan. Ya zamo sunan da aka sanya wa jarirai a yankuna biyar cikin tara na Ingila, sannan na 57 a Wales.
Haka nan sauran yadda ake rubuta sunan, kamar Mohammed, shi ne na 21 inda aka sa wa jarirai 1,760, sai kuma Mohammad a matsayin na 53, wanda aka sanya wa jarirai 986.









