Sudan ta kori ma’aikatan jakadancin Chadi daga Khartoum

0
205

Gwamnatin Sudan ta bai wa ma’aikatan diflomasiyyar Chadi wa’adin awa 72 su fita daga ƙasar a wani mataki na taɓarɓarewar hulɗa tsakanin ƙasashen biyu.

Kafar watsa labaran ƙasar ce ta bayyana haka ranar Lahadi.

Ta ambato hukumomin Sudan suna cewa jami’an diflomasiyyar na Chadi sun rasa martaba ta ci gaba da zama a Khartoum, don haka dole su tattara kayansu su fita daga ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Sai dai ba a bayyana sunaye da muƙaman jami’an diflomasiyyar da aka kora daga Sudan ba.

A nata ɓangaren, Chadi ta kori ma’aikatan diflomasiyyar Sudan da suka haɗa da babban jami’in diflomasiyya a ofishin jakadancin Sudan da ke Chadi, da babban jami’in tsaron ofishin da kuma ma’aikata biyu, kamar yadda gwamnatin Chadi ta bayyana ranar Asabar.

KU KUMA KARANTA : Ƙasar Chadi ta kori ma’aikatan diflomasiyyar Sudan

An ɗauki matakin ne bayan wani babban jami’in sojin Sudan Janar Yassir al-Attaya ya yi “kalamai masu nauyi marasa dalili,” sannan shi ma ministan harkokin wajen Sudan ya maimaita su a wani gidan talbijin, in ji sanarwar da kakakin gwamnatin Chadi ya fitar.

“Waɗannan kalamai da jami’in gwamnatin Sudan suka yi a kan Chadi da gwamnatin ƙasarmu ba abu ne da za mu amince da shi ba , kuma suna tunzura jama’a sannan cike suke da wata kullalliya,” a cewar sanarwar.

Yaki ya barke a Sudan tun watan Afrilu tsakanin dakarun sojin kasar da na rundunar Rapid Support Forces (RSF) lamarin da ya yi sanadin kisan dubban mutane, sannan miliyoyi suka tsere daga gidajensu, ciki har da dubbai da suka tsallaka cikin Chadi.

Leave a Reply