Su wa suka kashe matashin ɗan soshiyal midiya a Kwara?

An tsinci gawar wani matashi ɗan shekara 27 ma’abocin amfani da kafafen sada zumunta, Yusuf Mubarak wanda aka bayyana ɓacewarsa a jihar Kwara.

An ce an yiwa Mubarak ganin ƙarshe ne a unguwar Sakatariyar Tarayya, kan titin Tarayya da ke Birnin Ilorin, da misalin ƙarfe 9:40 na dare, a ranar Laraba, 13 ga Satumba, 2023.

Tun daga wannan lokacin, ba a sake jin ɗuriyar ɗalibin Jami’ar Jihar Nasarawa ba.  Sai dai an tsinci gawarsa a unguwar Unity Road da ke cikin birnin Ilorin a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba.

Wani ɗan jarida mai suna Saeed Tijjani ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya wallafa a Facebook.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Kaduna, sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da huɗu

“Ya ku ‘yan uwa da masoyan Yusuf Mubarak, muna baƙin cikin sanar da tabbatar da rasuwar ɗan uwanmu da aka bayyana ɓacewarsa jiya. Allah Ya karɓi komawarsa gareshi, Ya gafarta masa zunubansa, Ya saka masa da Aljannah, kuma ya dawwama da dukkan abin da ya bari.” Inji shi.

Da yake mayar da martani game da faruwar lamarin, Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya umurci hukumomin tsaro da su gano bakin zaren lamarin tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban ƙuliya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *