SSANU da NASU sun yi zanga-zangar lumana a jami’ar ABU

0
95
SSANU da NASU sun yi zanga-zangar lumana a jami'ar ABU

SSANU da NASU sun yi zanga-zangar lumana a jami’ar ABU

Daga Idris Umar, Zariya

Da safiyar ranar Talata ne ƙungiyar manya da ƙananan ma’aikatan jami’ar Ahmadu Bello Zariya SSANU da NASU suka gudanar da zanga-zangar ƙorafi a cikin harabar jami’ar dake Samaru Zariya.

Jerin zanga-zangar sun fara ne daga dandalin Mamman Kwantagora zuwa babbar hanyar mashigar jami’ar.

Kwamaret Muhammad Yunusa shugaban ƙungiyar ta SSANU kuma shi ne shugaban gamayyar ƙungiyoyin da ke fafutu kar.

 

A yayin da ya ke gudanar da jawabinsa a cikin dubban ‘ya’yan ƙungiyar da suka taru don nuna damuwarsu ga halin da suke ciki da ya sa suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu a wannan ranar.

Kwamaret Yunusa ya ce sun fito ne saboda bin umurnin uwar ƙungiyar su ta ƙasa domin nuna damuwarsu a kan rashin cika alƙawarin da gwamnatin tarayya take yi game da Haƙƙoƙin su da suke binta da ya haɗa albashi da wasu alawas-alawus da suke bi na watanni 4 da suka gabata.

KU KUMA KARANTA: An yi zanga-zangar neman ƙasashen Musulmai su tura sojoji don taimaka wa Falasɗinawa a Gaza

Kwamaret Ynusa yace a kwanakin baya sun je yajin aikin bisa matsaya da aka yi da gwamnatin tarayya ya sa suka dawo da nufin za a share masu hawayaensu yace amma abin mamaki sai aka sharewa wasu hawayensu amma su aka yi ko’in-kula da su koken nasu yace, hakan bai dace ba.

Don haka shugaba yace “Wannan fitowar ta nuna gargaɗine idan ba’a biya mu haƙƙinmu ba, gaba kaɗan zamu je yajin aikin gargaɗi in ba su ɗauki mataki bayan mu haƙƙoƙinmu ba to tabbas ƙungiya za ta ɗauki mataki na ƙarshe na zuwa yajin aiki mafi girma na ƙasa baki ɗaya” inji shi

Ƙarshe ya yi ƙira ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinibu da cewa ya dena kula masu hana ruwa gudu da ke ƙoƙarin cin amanar ƙasa da ke cikin gwamnatin sa .

Ya ce ƙungiyar SSAN da NASU ƙungiyoyi ne da suke riƙe da ƙasa baki ɗaya domin duk wanda zai yi aikin gwamnati musamman Jami’a to sai ya biyo ta gaban kungiyar saboda muhimmanci su

Kuma ya ƙarƙare da yin jinjina ga gamayyar ƙungiyoyin da suka bayar da haɗin kai suka fito suka nuna goyon baya tare da bin duk dokokin ƙungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here