Gwamnatin jihar Anambara ta sanar da rufe makarantar ‘Blessed Wisdom Model School’ da ke Ide Drive, Federal Housing Estate, Onitsha, sakamakon bulala da aka yi wa wata ɗaliba ‘yar shekara biyu.
Kwamishiniyar ilimi ta jihar Ngozi Chuma-Udeh ce ta sanar da hakan a ranar asabar ɗin da ta gabata, biyo bayan wani rahoto da aka samu na cewa wata ɗaliba mai suna Ifechukwu Egbuninwe mai shekaru biyu ta samu munanan raunuka a jikin ta, biyo bayan yi masa bulala.
Misis Chuma-Udeh ta ce: “A cewar rahoton, wadda aka daka ɗin ta karya hannunta kuma ta samu raunuka a harshenta a wani yanayi da har yanzu ba a bayyana mata ba.
KU KUMA KARANTA: An ɗaure matashiya a gidan yari, saboda ta yi duka a Malamar ta
“Rahoton ya kuma bayyana cewa mai makarantar ba ta tuntuɓi iyayen ɗalibar ba, don sanar da su raunin da ta samu ba kuma ba a yi mata agajin gaggawa ba a lokacin da ta samu wannan rauni.
“Matar ta ka sa tuntuɓar dangin ɗalibar a kowane lokaci don tabbatar da lafiyarta.
Haka kawai suka ci gaba da harkokinsu na makaranta kamar rayuwar ɗalibi ba ta da wani abu.”
Kwamishinan ya yi Allah wadai da halin da mahukuntan makarantar Blessed Wisdom Model suke yi ga rayuwar ɗan Adam da kuma rashin biyayyar da mai gidauniyar da ta ƙi amsa gayyatar ta.
“Kowane yaro na jiha ne, ba za mu iya lamuntar rashin kula da rayuwar ɗan Adam ba.
Don haka ne a ranar Juma’a muka gayyaci mai makarantar ta zo ta bayyana abin da ya faru.
“Yarinyar da iyayenta da lauyansu sun hallara amma mai makarantar ta ki zuwa.
Wannan rashin bayyanar da ya sa aka yanke shawarar rufe makarantar.
“An umurci jami’an rundunar haɗin gwiwa ta jihar Anambara da su tabbatar da bin ƙa’idar rufewar.
Makarantar ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai Gwamna ya ba da umarnin akasin haka,” in ji ta.
A halin da ake ciki, Misis Chuma-Udeh ta kafa wani kwamiti mai mutane bakwai don gudanar da bincike kan lamarin yayin da ta shawarci mai gidan da ta yi ƙoƙarin bayyana a gaban kwamitin.
A cewarta, rashin bayyana a gaban kwamitin zai sa a kama su da kuma gurfanar da su gaban ƙuliya.
[…] KU KUMA KARANTA: Soludo ya rufe makaranta a Onitsha saboda zaluntar ɗaliba ‘yar shekara biyu […]