Sojojin Nijar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 29
Rundunar Sojin Nijar ta yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 19 a yankin Tillaberi na ƙasar.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 20 ga Disamba a Karey-Goussou da misalin ƙarfe 2:00 na rana.
Maharan sun far wa sojojin ne a kan babura kwatsam a lokacin da suke sinitiri a yankin.
Duk da cewa hari harin na ba-zata ne suka kai wa sojojin, amma sojojin sun yi ƙoƙari inda suka kashe ‘yan ta’addan 29 tare da ƙwace baburansu huɗu da ƙwace musu makamai da wasu kayayyakin sadarwarsu.
Sai dai kuma sojojin ƙasar huɗu sun rasa rayukansu sakamakon wannan harin na ‘yan ta’adda.
Nijar na daga cikin ƙasashen Yammacin Afirka waɗanda ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda musamman masu iƙirarin jihadi.
Ƙasashen da ke makwabtaka da Nijar ɗin irin su Najeriya da Burkina Faso da Mali su ma suna fama da ‘yan ta’addan.
KU KUMA KARANTA: Wani harin bam ya kashe sojojin Nijar 6
Yankunan da ke kan iyaka tsakanin Nijar da Mali da Burkina Faso sun kasance mafakar ‘yan ta’adda da ke da alaƙa da Daesh da Al Qaeda, waɗanda suka yi yaƙi da gwamnati.
Ko a makon da ya gabata sai da ‘yan ta’addan suka kashe aƙalla mutum 39 a wasu hare-hare biyu da suka kai yammacin ƙasar.