Sojojin Nijar sun soke dokar da ta haramta tafiya ci-rani Turai

0
155

Sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun soke dokar da ta taimaka wurin rage kwararar ‘yan ƙasashen Yammacin Afirka zuwa Turai musamman mazauna karkara waɗanda ke fama da matsin tattalin arziki da suka daɗe suna dogara da ci-rani.

An yi dokar ne a 2015 wadda ta haramta jigilar jama’a ta cikin Nijar ba bisa ka’ida ba don ratsawa ta Bahar Rum daga Afirka zuwa Turai.

Gwamnatocin ƙasashen Turai sun sha kokawa kan matsin lambar da suke fuskanta a cikin gida sakamakon kwararar ‘yan ci-rani daga Afirka.

Sojojin Nijar, waɗanda suka yi juyin mulki a watan Yuli, sun soke dokar ne a ranar Asabar amma sun sanar da ita ranar Litinin da daddare a gidan talabijin.

Gwamnatin mulkin sojan tana sake nazarin alakarta da tsofaffin ƙawayenta na Ƙasashen Yamma waɗanda suka yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar.

KU KUMA KARANTA: Nijar ta yi wa dubban yara riga-kafin cutar sarƙewar numfashi

Ana ganin gwamnatin Nijar ɗin ta ɗauki wannan matakin ne domin ƙara samun goyon baya a cikin gida.

Adadin ‘yan ci-ranin da ke shiga ta cikin Nijar, wadda ita ce ƙasar da aka fi ratsawa da yada zango a tafiya zuwa Turai, ya ragu matuka a tsawon shekaru sakamakon wannan dokar. Sai dai a baya dokar ta sa iyalai da dama sun shiga wahala musamman waɗanda ke ƙauyuka da garuruwan da ke kan hanya waɗanda suka rika bayar da mafaka da abinci da sayar da kayayyakin mota ga waɗanda ake zargi da safarar jama’a.

Sakamakon wannan doka da aka saka, Tarayyar Turai ta kaddamar da wata gidauniya ga Afirka a 2015 ta euro biliyan biyar, inda aka ware kuɗin domin kawar da matsalolin da ke tattare da ci-rani, sai dai da dama suna ganin wannan matakin bai isa ba.

Rashin aikin yi ya ƙaru a birane irin su Agadez, wanda wuri ne da ya yi suna ga masu tafiya ta cikin Sahara.

Leave a Reply