Sojojin Nijar sun saki ɗan Mohamed Bazoum

0
130

Wata kotun soji a Jamhuriyar Nijar ta saki Salem, ɗan hambararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

Kotun ta CNSP ta bayar da sanarwa Salem Bazoum ne a wata takarda da ta fitar ranar Litinin da maraice.

Sanarwar ta ce an miƙa shi ga Ministan Harkokin Waje na Togo Robert Dussey, kuma tuni suka fita daga ƙasar zuwa birnin Lome.

An yi wa Salem, mai shekara 23, ɗaurin-talala tare da mahaifansa a gidan shugaban ƙasa da ke Yamai tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Bazoum a watan Yulin da ya gabata.

Juyin mulkin, wanda shi ne na takwas da sojoji suka yi a Yammaci da Tsakiyar Afirka tun daga 2020, ya jawo wa ƙasar baƙin-jini, har ya kai ga ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta sanya mata takunkumi yayin da kuma ƙasashen duniya suke ta ƙiraye-ƙirayen a Bazoum tare da mika mulki ga gwamnatin dimokuraɗiyya.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan uwan Bazoum ba su ji ɗuriyarsa ba tun 18 ga watan Oktoba

Kotun ba ta yi bayani game da makomar Bazoum da mai ɗakinsa ba.

A watan jiya, kotun ECOWAS ta ce ɗaurin-talalar da aka yi wa Bazoum da iyalansa ya ƙeta doka inda ta buƙaci a sake shi sannan a mayar da shi kan mulki.

Kotun, wadda ba a daukaka ƙara kan hukuncin da ta yanke, ta bai wa sojojin Nijar wa’adin wata ɗaya su bayyana mata yadda za su aiwatar da umarninta, a cewar lauyoyi.

Sojojin suna tuhumar Bazoum da ɗansa Salem bayan juyin mulkin da suka yi ranar 26 ga watan Yuli. An zargi Salem da haɗa baki wajen yunkurin yin tarnaki ga hukumomi da tsaron Nijar.

An katse ruwa da lantarki a gidan da Bazoum da iyalansa suke ciki tun da sojoji suka yi masa juyin mulki, a cewar jami’an jam’iyyarsa da kuma ‘yan’uwansa.

A baya, lauyansa ya ce an hana shi zuwa kotu domin yin ƙarar sojojin da suka yi juyin mulki.

Leave a Reply