Sojojin Nijar sun amince da sharuɗɗan miƙa mulki ga gwamnatin farar-hula

0
192

Sojojin Nijar sun amince da sharuɗɗan miƙa mulki ga gwamnatin farar-hula, kuma za su gabatar da tsarinsu na yin haka ga ƙungiyar ECOWAS, a cewar wani jam’in diflomasiyyar ƙasar Togo wadda ke shiga tsakanin ɓangarorin biyu.

Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey ne ya bayyana haka ranar Alhamis a wata hira da gidan talbijin na Jamhuriyar Nijar.

Ya ce an cim ma yarjejeniya “game da lokaci da kuma tsare-tsaren” miƙa mulki a ganawarsu da Firaiministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine da ministan harkokin waje Bakary Yaou Sangare.

“Mun shirya gabatar da tsare-tsare… ga shugabannin ƙasashen da ke shiga tsakani da kuma Majalisar ECOWAS,” in ji shi.

ECOWAS ta sanya wa Nijar jerin takunkumai ciki har da na rufe kan iyakokin mambobinta da katse lantarki da ake ba ta daga Najeriya da kuma dakatar da ƙasar daga harkokin kuɗi na ƙungiyar, tun da aka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Takunkuman da aka sanya wa Nijar da kuma cire ta daga cikin harkokin ƙasashen duniya sun jefa ta cikin ƙarin matsin tattalin arziki.

KU KUMA KARANTA: Amurka na son ci gaba da ƙawance da Nijar kan tsaro da haɗin kai

A watan Oktoba, shugabannin sojojin sun sanar da rage kashi 40 cikin ɗari na kasafin kuɗin ƙasar na 2023 “sakamakon takunkuman da ƙasashen duniya da na lardi suka sanya mana”.

A taron ECOWAS na ranar Lahadin da ta gabata, shugabanninta sun gindaya wa sojojin Nijar sharuɗɗa kafin su cire musu takunkumai.

Sun naɗa kwamitin mutum uku na shugabannin ƙasashen Togo da Benin da Saliyo domin tattaunawa da sojojin Nijar da kuma bibiyar yadda za su cika waɗannan sharuɗɗan.

A baya dai, sojojin na Nijar sun ce za su iya kwashe shekara uku a kan mulki kafin su sauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here