Sojojin Nijar na zargin Faransa na shirin kai hari don kuɓutar da Bazoum

1
316

Daga Ibraheem El-Tafseer

Sojojin sun yi zargin cewa Faransa ta haɗa baki da wasu ‘yan Nijar domin ta yi amfani da ƙarfin soji wajen kuɓutar da Mohamed Bazoum.
Bazoum Mohamed ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro a Yammacin Afirka.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun zargi Faransa da ƙoƙarin yin “amfani da ƙarfin soji” domin sake mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa a yayin da ake ci gaba da matsa musu lamba su koma bariki.

Sun yi zargin ne ranar Litinin a wani jawabi da suka yi a gidan talabijin na ƙasar.

KU KUMA KARANTA: An tabbatar da Sojoji sun yi juyin mulki a Nijar

“A ƙoƙarinta na yin amfani da kowace hanya da ta haɗa da ƙarfin soji a kan Jamhuriyar Nijar, Faransa ta haɗa baki da wasu ‘yan Nijar inda suka yi taro da shugaban Zaratan Sojin Nijar domin samun amincewa a siyasance da kuma ta fuskar soji,” in ji sanarwar da suka fitar.

Da ma dai ranar Lahadi Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sha alwashin ɗaukar mataki “nan take kuma mai kaushi” idan aka kai hari kan ‘yan ƙasarsa a yayin da dubban masu zanga-zanga suka taru a wajen ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai.

A makon jiya ne Janar Abdourahamane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban Nijar kwanaki kaɗan bayan sojojin sun yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki.

A jawabin da ya yi a lokaci, ya gargaɗi ƙasashen duniya da ka da su kuskura su tsoma baki kan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar idan ba haka ba komai zai iya faruwa.

Ƙasashe da manyan ƙungiyoyin duniya sun yi Allah wadai da juyin mulkin sannan suka sha alwashin ƙin amincewa da sojojin na Nijar.

Ƙungiyar ƙasashen raya tattalin ariziƙin Afirka ta Yamma ECOWAS ta bai wa sojojin wa’adin kwana bakwai su mayar da Bazoum kan mulki ko kuma ta ɗauki matakin soji a kansu.

1 COMMENT

Leave a Reply