Sojojin Najeriya sun tarwatsa masana’antar ƙera bindigogi a Taraba

0
283

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce dakarun ‘Operation Whirl Stroke’ sun kai samame a wata masana’antar ƙera makamai da ke Wukari a Taraba tare da cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne.

Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Musa Ɗanmadami, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce sojojin sun yi aiki da sahihan bayanan sirri.

Manjo Janar Ɗanmadami, ya ce a ranar Juma’ar da ta gabata ne sojojin suka ƙwato GPMG guda biyu, KPM ɗaya, bindigu AK 47 guda huɗu, bindigu guda uku, PKT ɗaya, alburusai 9mm biyar, alburusai 7.63 x 54 guda biyu, harsashi guda bakwai da kuma wasu sassa na bindigu daban-daban.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe ‘yan bindiga bakwai, sun kama biyu a Zamfara

Ya ce an miƙa masu laifin da aka kama da makamai da alburusai ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki.

“Babban kwamandan sojojin ya yabawa sojojin na ‘Operation Whirl Stroke’ tare da ƙarfafawa jama’a gwiwa da su baiwa sojoji bayanai masu inganci kuma kan lokaci kan ‘yan ta’adda da duk wasu ayyukan aikata laifuka a yankinsu,” in ji shi.

Leave a Reply