Hedikwatar tsaro ta ce dakarun ‘Operation Delta Safe’ sun lalata haramtattun wurare tace man fetur 36 tare da kama wasu mutane 22 da ake zargin ɓarayin mai ne a cikin makonni biyu da suka gabata.
Darakta mai kula da ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo janar Edward Buba, ya bayyana haka ne a yayin da yake bayar da ƙarin haske kan ayyukan rundunar a wani taron manema labarai na mako biyu a ranar Alhamis a Abuja.
Buba ya ce, sojojin sun kuma lalata ramuka 61, kwale-kwalen katako 32, tankunan ajiya 87, motoci uku, tanda 126 na dafa abinci, injin fita guda uku, jirgin ruwa mai sauri ɗaya, babura biyu, janareta ɗaya da injinan fanfo guda biyu. Ya ce sojojin sun kuma ƙwato litar ɗanyen mai lita 310,700, lita 14,675 na Automotive Gas Oil, lita 49,000 na kananzir Dual Purpose, makami ɗaya da alburusai uku.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun hanyoyin tace mai 57, sun kama 16
A cewarsa, “Sojoji a ranar 24 ga watan Yuli, sun kama wani kwale-kwalen katako da ke ɗauke da lita 1000 da ake zargin satar ɗanyen mai ne a yankin Wellhead Cluster Opukushi a ƙaramar hukumar Ekeremor ta jihar Bayelsa.”
A yankin Kudu maso Gabas, dakarun Operation UDO KA sun kai samame kan sansanonin da maɓoyar ‘yan asalin yankin Biafra/Eastern Security Network a jihohin Abiya da Anambara.
Ya ce sojojin sun kuma kama wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, tare da kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato makamai da alburusai a ƙaramar hukumar Onitsha ta Arewa da ke Anambara.
“A yayin gudanar da samamen, sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya ɗauke da bindigogi 35 na musamman mai nauyin 7.62, bindigogin fanfo guda shida, bindigar gida ɗaya, bindigar ɗane ɗaya, bam ɗin hannu guda ɗaya, motoci huɗu, babura tara, adduna 925. da kuma masu kaifi 151.
“Sauran sun haɗa da sikila 1,080, rigar ‘yan sandan Najeriya da takalma, rigar IPOB/ESN, mai magana ƴaya, rigar ruwan sama da takalmi da sarƙa.
Sojojin sun kuma kama wasu ‘yan bindiga uku tare da kuɓutar da mutane tara da aka yi garkuwa da su.
“Gaba ɗaya, sojoji za su ci gaba da ɗorawa wajen tunkarar ƙalubalen tsaro kuma za su ci gaba da yaƙar masu laifin don miƙa wuya.
“Ana sa ran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa za su ci gaba da baiwa sojoji goyon baya, kuma za su tsaya tare da sojoji don fatattakar masu aikata wannan munanan ayyuka daga cikinmu. Tare za mu iya fitar da su,” inji shi.
[…] KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun wurare tace mai 36, sun kama mutane 22 a yankin Neja Delta […]