Sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 254 a cikin mako guda

0
136

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta ce sojojin ƙasar sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda 254 da kuma kama 264 a cikin mako guda a faɗin ƙasar.

Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron Manjo Janar Edward Buba ne ya tabbatar da hakan a wani taron watsa labarai a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa a samamen da jami’an tsaron suka kai a faɗin ƙasar, sun ceto mutum 73 waɗanda aka yi garkuwa da su.

A yankin kudu maso kudancin Nijeriya, sojojin ƙasar sun samu nasarar ƙwato gangar mai 20,643 daga hannun ɓarayin mai wanda kuɗin man ya kai kimanin naira biliyan 2.6.

Sojojin sun ce duk a cikin mako guda, sun yi nasarar ƙwato makamai 5,083 daga hannun ƴan ta’addan da kuma tsabar kuɗi naira 748,430.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindigar da suka addabi Birnin Gwari

Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da motoci 18 da babura 40 da wayoyin hannu 74 da ɗumbin harsasai da bindigogi.

Matsalar tsaro a Najeriya na ƙara ƙamari duk da jami’an tsaron ƙasar suna iƙirarin samun nasara.

Domin ko a cikin makon nan sai da sojojin ƙasar suka ce sun gano wani waje da ake ƙera makamai a Jihar Filato tare da gano tarin makamai da harsasai.

Haka kuma a makon da ya gabata sojojin sun ce sun kama wani kasurgumin dan bindiga da ake nema wanda yake da hannu a safarar makamai ga masu laifi a jihar Taraba da ma wasu sassan kasar.

Arewa maso gabashin Najeriya da kuma arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin wuraren da ƴan ta’adda suka fi addaba.

Leave a Reply