No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ƴan bindiga huɗu a ƙauyen Kampanin Doka a ƙaramar hukumar birnin Gwari na jihar Kaduna.

Wata sanarwa da sojojin suka fitar, ta ce sun samu nasarar kashe ƴan bindigar ne a ranar 1 ga watan Nuwamba a wani samame da suka kai ƙauyen.

Sojojin sun ce sun ƙwato bindigar AK 47, da harsasai, da adda guda ɗaya, wayar tarho, da kuma babura 14 daga hannun ɓata-garin.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga uku da ƙwato bindigogi a Kaduna

A wani samame na daban da sojojin suka yi ranar 2 ga watan Nuwamba a ƙauyen Sabon Sara, sun ce sun kashe wani ɗan bindiga ɗaya, wasu kuma suka tsere da raunukan bindiga, bayan da wasu manoma suka kai musu rahoton ganin ƴan bindigar.

“Mun ƙwato bindigar AK 47 guda biyu, yayin da ɗaya daga cikin manoman da ya samu rauni muka ɗauke shi zuwa wani asibitin sojoji da ke kusa don yi masa magani,” in ji sanarwar sojojin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...