No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sojojin Najeriya sun kama ‘kayan haɗa bama-bamai’ a jihar Yobe

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi nasarar kama motoci maƙare da kayayyakin da take zargi na harhaɗa bama-bamai ne da ake shirin tsallakwa da su Jamhuriyar Nijar.

A ranar 16 ga watan Satumba dakarun rundunar musamman ta Operation Haɗin Kai ne suka kama wata babbar mota ɗauke da buhuhunan takin zamani 700 a kan hanyar Nguru zuwa Gashuwa na jihar Yobe.

KU KUMA KARANTA: Dole sojojin Najeriya su koyi harsunan gida don samun sahihan bayanan sirri — COAS

“A wannan ranar ce binicke ya nuna cewa motar na ɗauke da buhun takin zamani 700, wanda ake haɗa bama-bamai, da ƙwayoyi daban-daban, waɗanda aka ɓoye cikin kaya,” a cewar wata sanarwa da Kanal Sani Uba ya fitar.

“Bayanai sun nuna cewa an yi niyyar kai kayan ne Jamhuriyar Nijar, abin da ke nuna ayyukan safarar kayan ta’addanci tsakanin ƙasa da ƙasa.”

A cewarsa, sun kuma kama wata mota ɗauke da farantan samar da lantarki daga hasken rana da sauran kayayyaki, waɗanda bayanai suka nuna “‘yanta’adda na shirin tattara kayayyaki dinka wa mayaƙansu kakin soja ne”.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...