Sojojin Najeriya sun gano wurin da IPOB ke haɗa jirage marasa matuƙa

0
225

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta gano wani wuri da ƴan ƙungiyar IPOP ke haɗa jirgi maras matuƙi masu ɗauke da makamai.

Rundunar ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata inda ta ce ta gano wurin ne a Ƙaramar Hukumar Aniocha ta Kudu da ke Jihar Delta.

Rundunar sojin ta bayyana cewa bayanan sirrin da suka tattara sun nuna cewa ƴan ta’addan na IPOB na amfani da wurin haɗa jiragen marasa matuƙa domin kitsa kai hare-hare a cikin al’ummomin da ba su ji ba su gani ba.

Sojojin sun ce a yayin da suka kai samame wurin haɗa jiragen, sun fuskanci turjiya daga yan IPOB ɗin sai dai bayan musayar wuta, sun tarwatsa su inda har suka kashe biyu daga cikinsu.

Sojojin sun ce daga cikin abubuwan da suka samu a wurin haɗa jiragen akwai tulin makamai iri daban-daban da bama-bamai da samfuran jiragen marasa matuƙa.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe  gomman sojojin Mali

Haka kuma sojojin sun kama mayaƙan ƙungiyar maza huɗu da mata biyu.

Ƴan ta’addan IPOB na daga cikin waɗanda ke kai hare-hare musamman kan jami’an tsaro a kudu maso kudancin Nijeriya.

Sau da dama sun sha ƙona ofisoshin yan sanda da ƙwace musu makamai musamman a jihohin Abiya da Anambara da Inugu da Imo.

Jagoran ƙungiyar Nnamdu Kanu ya shafe lokaci mai tsawo a tsare inda yake shari’a da gwamnatin Najeriya kan zarge-zarge da dama wadanda akasarinsu na ta’addanci ne.

Leave a Reply