Sojojin Najeriya sun banka wa jirgin ruwan satar ɗanyen man fetur wuta

1
366

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jami’an tsaron Najeriya sun cinna wa jirgin ruwan dakon mai da aka kama ɗauke da ɗanyen mai na sata wuta a yankin Escravos na Naija-Delta.
Irin haka shi ne karo na biyu a cikin wata tara.

A ranar Litinin ne kamfanin man fetur na ƙasar, NNPCL ya sanar da kama jirgin ruwan maƙare da ɗanyen man fetur.

Hukumomi sun ce jirgin wanda ke kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Kamaru, na ɗauke da ɗanyen mai lita 800,000, wanda ya sato daga wani yanki na jihar Ondo a kudancin Najeriya.

Jirgin, mallakin wani kamfani na Najeriya, hukumomi sun ce ya kwashe shekara 12 yana aiki cikin sirri.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe babban ɗan ta’adda da wasu mutane biyar a bodar Najeriya da Kamaru

Sai dai babu tabbaci ko an kwashe ɗanyen man kafin cinna masa wuta ko a’a.

Ɓangaren man fetur na Najeriya ya kwashe shekaru yana fama da rashawa da satar ɗanyen mai da kuma kafa matatun man fetur ba bisa ƙa’ida ba.

A shekarar 2022 gwamnatin Najeriya ta ce tana asarar sama da gangar mai lita 470,000 a kowace rana sanadiyyar ayyukan maɓarnata.

Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sha alwashin yaƙi da satar ɗanyen man fetur, wanda shi ne babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga na ƙasar.

1 COMMENT

Leave a Reply