Sojojin Najeriya sun ƙuɓutar da mutum 31 da aka yi garkuwa da su a Sokoto

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Hadarin Daji da ke aikinta a Arewa maso Yammacin Najeriya ta ce ta samu nasarar ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su a jihar Sokoto.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a ranar Laraba, ta ce an ceto mutanen ne a ranar litinin 21 ga watan Nuwamba bayan kai samame ƙauyen Alya Fulani da dajin Buani da ke ƙaramar hukumar Tangaza.

“Jajirtattun dakarun rundunar Hadarin Kaji ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut na ci gaba da kai zafafan hare-hare kan ‘yan ta’adda a yankunan da suke gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Yamma,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun sace ɗalibar UDUTH a hanyar Sokoto zuwa Shinkafi

Ta ƙara da cewa “an gano maɓoyar dukkan ƴan ta’addan tare da lalata su, lamarin da ya sa suka tsere suka kuma bar mutanen da suke garkuwa da su a wajen, kafin isar zaƙaƙuran dakarun.”

Daga nan sai dakarun suka wuce ƙauyen Goboro inda suka ceto wata mace ɗaya da aka yi garkuwa da ita, bayan guduwar ƴan bindigar da suka tsare ta sakamakon fin ƙarfinsu da sojojin suka yi.

Jihar Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Nijeriya da ƴan bindiga ke yawan kai hare-hare ƙauyukansu da kuma yin garkuwa da mutane.

Sai dai a baya-bayan nan hukumomin tsaron Najeriya suna cewa suna samun galaba sosai a kan ƴan bindigar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *