Sojojin Najeriya a Zamfara, sun ceto tsohon shugaban kwalejin ilimi da ɗansa

0
309

Rundunr sojin Najeriya ta ce ta ƙubutar da tsohon shugaban kwalejin ilimi ta tarayya da ke Gusau Dakta Hassan Abubakar Augie tare da ɗansa daga hannun masu garkuwa da mutane.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinsa na Tuwita, sun dakarunsu na rundunar Hadarin Daji da ke Mada ne suka kuɓutar da Dakta Augie tare da ɗansa a lokacin wani sintiri da suka gudanar da a kan hanyar Shemori zuwa ‘Yandoto.

Sanarwar ta ce dakarun sun fatattaki ‘yan bindigar masu yawa, inda suka yi musayar wutar da su.

Sojojin sun ce ‘yan bindigar sun gudu zuwa cikin daji bayan da suka ji wuta daga ɓangaren sojojin, tare da barin mutanen biyu da suka sacen.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 38, sun kama mutane 242 – Hedikwatar tsaro

Binciken farko ya nuna cewa an sace mutanen biyu ne a daren ranar Alhamis a gidan Dakta Augie, inda aka tafi daji da su inda suka ci gaba da tsare su, har zuwa lokacin da sojojin suka isa wajen.

Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato babura biyu na ‘yan bingidar a lokacin gumurzun.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da rikice-rikicen ‘yan bindiga da ke sace mutane domin neman kuɗin fansa

Leave a Reply