Daga Ibraheem El-Tafseer
Sojojin mulkin Gabon sun naɗa Raymond Ndong Sima a matsayin firaminista na riƙon-ƙwarya.
Mutumin mai shekara 68 masanin tattalin arziƙi ne kuma cikakken mai adawa da hamɓararren Shugaba Ali Bongo, duk da cewa ya yi aiki matsayin firaministan ƙasar daga 2012 zuwa 2014.
Ya so ya shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen da aka kammala amma ya yanke shawarar mara wa babban ɗan takarar adawa Albert Ondo Ossa baya.
KU KUMA KARANTA: Ƙasar Gabon ta sake buɗe iyakokin ƙasar – Sojoji
Tun farko, sojojin mulkin sun ce sun saki Ali Bongo daga ɗaurin talalar da suka yi masa tun bayan da suka hamɓarar da gwamnatinsa.
Janar Brice Oligui Nguema ne ya jagoranci juyin mulkin, wanda kuma aka rantsar a matsayin shugaban ƙasa na riƙon-ƙwarya ranar Litinin da ta wuce.