No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sojojin Isra’ila da mayaƙan ƙungiyar Hezbollah na Lebanon sun yi artabu ta kan iyakar ƙasashen biyu a yau Asabar, inda kowanne ɓangare ke ikirarin samun nasara a farmakin da ya ƙaddamar.

Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya da shugaban ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah ya yi gargaɗin cewa, yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da mayaƙan Hamas a Zirin Gaza, ka iya rikiɗewa zuwa wani gagarumin rikici a yanƙin gabas ta tsakiya muddin Isra’ilar ta ci gaba da kai wa Falasɗinawa hari.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kai hari kan motocin asibiti a kusa da asibitin Al Shifa na Gaza

Isra’ila ta ce ta mayar da martani saboda makamin atilari da aka cillo mata daga Lebanon, amma babu wanda ya rasa ranta daga cikin jama’arta a cewarta.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...