Sojojin Isra’ila da mayaƙan ƙungiyar Hezbollah na Lebanon sun yi artabu ta kan iyakar ƙasashen biyu a yau Asabar, inda kowanne ɓangare ke ikirarin samun nasara a farmakin da ya ƙaddamar.
Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya da shugaban ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah ya yi gargaɗin cewa, yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da mayaƙan Hamas a Zirin Gaza, ka iya rikiɗewa zuwa wani gagarumin rikici a yanƙin gabas ta tsakiya muddin Isra’ilar ta ci gaba da kai wa Falasɗinawa hari.
KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kai hari kan motocin asibiti a kusa da asibitin Al Shifa na Gaza
Isra’ila ta ce ta mayar da martani saboda makamin atilari da aka cillo mata daga Lebanon, amma babu wanda ya rasa ranta daga cikin jama’arta a cewarta.