Sojojin Isra’ila sun sace Falasɗinawa 300 daga asibitin Gaza

0
126

Sojojin Isra’ila sun yi awon gaba da Falasɗinawa kusan 300 a ci gaba da kutsawa da suke yi cikin asibitin Al Shifa da ke birnin Gaza.

Wata sanarwa ta ce “sojoji sun kama kusan mutum 300 tare da kawar da ƴan ta’adda da dama.

KU KUMA KARANTA: Blinken zai je Saudiyya da Masar domin tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza

Sojojin sun kai harin ne a ranar Litinin da ta gabata, wanda ke dauke da dubban marasa lafiya da suka jikkata da kuma mazauna wurin.

A shekarar da ta gabata a watan Nuwamba, Isra’ila ta kai hari a asibitin, lamarin da ya tayar da hankalin kasashen duniya.

Tel Aviv ta yi iƙirarin karya cewa mayakan Hamas na amfani da asibitin wajen ayyukan soji. Kwanaki bayan haka ya bayyana a fili cewa sojojin Isra’ila a haƙiƙa suna magana ne a kan tudun da ke ƙarƙashin ginin da Isra’ila ta gina a shekarar 1983 a lokacin da ta yi wa Gaza mummunar mamayar.

Leave a Reply