No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Litinin ta kama Falasɗinawa 28 a wasu jerin samamen da ta kai Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kungiyoyin kula da fursunoni suka tabbatar.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da hukumar kula da fursunonin Falasɗinawa ta fitar ta ce akwai yara da dama daga cikin wadanda ake tsare da su a hare-haren da aka kai a garuruwan Jenin, Jericho, Ramallah, Bethlehem, Hebron, da Qalqilya.

KU KUMA KARANTA: An kama mutum 34 lokacin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka

Ana zaman ɗar ɗar a Gabar Yamma da Kogin Jordan tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da kazamin farmakin soji a zirin Gaza, inda kusan mutum 35,000 suka mutu sakamakon harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...