Sojojin Isra’ila sun ce, ba za su ci gaba da yaƙi ba, idan har…
Daga Ibraheem El-Tafseer
Aƙalla sojojin Isra’ila 130 suka rubuta wasiƙa aa gwamnatin ƙasar cewar ba za su ci gaba da yaƙi ba, muddin hukumomin ƙasar ba za su ɗauki matakin kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tun daga ranar 7 ga watan Oktobar bara ba.
A wata wasiƙar da suka rubuta ta ranar 9 ga wannan watan Oktoba, sojojin da waɗanda aka ƙira domin yiwa ƙasar yaƙi sun ce sun fahimci gwamnatin ƙasar ba ta son kawo ƙarshen yaƙin domin gudanar da zaɓe.
Ɗaya daga cikin sojojin ya ce tun da babu wani ci gaba wajen kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su, saboda haka babu dalilin ci gaba da wannan yaƙin da ƙasar ke yi. Sojan ya ce wannan wani matsayi ne ya ɗauka na bijirewa gwamnatin ƙasarsa saboda yadda ta kai matakin ƙarshe na yaudara.
KU KUMA KARANTA: Netanyahu ya tsallake rijiya da baya – Israila
Sojan ya ce da da gaske ake yi wajen kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su, da tuntuni an yi nasara, amma ana tsawaita yaƙin ne domin ƙin gudanar da zaɓe, matakin da zai bai wa (firaminista) damar ci gaba da zama a karagar mulki.
Rahotanni sun ce wasiƙar ta harzuƙa gwamnati wadda ta dakatar da wasu daga cikin sojojin.