Sojojin Isra’ila sun amince su kwashe jarirai daga babban asibitin Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta amince ta kwashe jarirai daga babban asibitin Gaza, al Shifa, inda halin da marasa lafiya ke ciki yake ƙara taɓarɓarewa saboda yaƙin da sojojin ke gwabzawa da Hamas a titunan da ke kusa da asibitin.

Kakakin rundunar ya ce za a kwashe jariran zuwa wani waje da babu barazanar tsaro, amma bai bayyana cikakken tsarin da aka yi a kai ba.

Likitoci a asibitin al Shifa sun ce wuta na ci a ginin, kuma marasa lafiya na fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin samun kulawar da ya kamata.

Isra’ila dai ta musanta cewa itace ta kai hari a asibitin, duk da cewa a baya ta yi iƙirarin cewa mayaƙan Hamas suna ɓoye a cikin asibitin.

KU KUMA KARANTA: Yaƙin Gaza: Tinubu ya buƙaci a gaggauta tsagaita wuta

Isra’ilan ta kuma bayyana cewa ta yi tanadin hanyar ficewa ga mutanen da ke son tserewa.

Lamurra na ƙara taɓarɓarewa a Gaza, yayin da dakarun Isra’ila ke ƙara kutsawa yankin da ke fama da ƙarancin abinci da mai, ga kuma rashin lantarki.

Sojin Isra’ila sun ce za su fara kwashe jariran da ke asibitin ne a ranar Lahadi, biyo bayan buƙatar hakan da mahukunta asibitin suka gabatar.

Daniel Hagari shi ne kakakin dakarun tsaron Isra’ila.

Ya ce: “Muna magana kai-tsaye tare da mahukunta asibitin. Ma’aikata a asibitin Shifa sun buƙaci mu kwashe jariran da ke asibitin don kai su wani asibtin da babu ƙalubalen tsaro. Za mu bayar da tallafin da ake buƙata.”

Likitoci a asibitin al-Shifa dai sun yi gargaɗin cewa masu jinya za su fara mutuwa saboda rashin samun kula, cikin su kuma harda jarirai.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *