Sojojin gwamnatin Habasha sun sake ƙwace ikon birnin Lalibela

0
203

Birnin Lalibela a yankin arewa na ƙasar Habasha, ɗaya daga cikin birane dake kumshe da mujamiu ya koma hannun dakarun Gwamnati, rahotanni daga yankin na bayyana cewa mayaƙan sa kai da aka sani da sunan “Fano’ sun fice daga garin cikin dare vayan mamaye gari na wani lokaci.

A baya dai mayakan sa kai  sun goyi bayan sojojin Habasha tsawon shekaru biyu na rikici tsakaninta da hukumomin ‘yan tawaye na yankin Tigray, wanda ya kare tare da yarjejeniyar da aka sanya hannu a watan Nuwamba 2022 a Pretoria na ƙasar Afirka ta Kudu.

Sai bai da dama na kallon wannan yarjejeniya a matsayin koma baya ga kawance yayin da ‘yan ƙabilar Amhara ke zaman doya da man ja da mutanen Tigray.

Yarjejeniyar ta ƙara dagula al’amura a yankin na Amhara, wanda ya kawo cikas ga tsarin hukumomin a ɓangaren da ya shafi  yunkurin kwance damarar sojojin yankin a watan Afrilu.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kama masu ƙera haramtattun makamai a Filato

Tsawon wani lokaci kafin wayewar gari,mayaka yan sa kai da aka sani da  Fano ne ke riƙe da mafi yawan garuruwan, sun haɗa karfi da sauren mayaƙa wajen barin garin,” in ji wani mazaunin garin wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro.

A ranar Laraba da yamma wasu mazauna yankin sun nuna cewa mayaƙan sa kai na ƙungiyar Fano ne ke iko da mafi yawan Lalibela kuma an sake tura dakarun gwamnatin tarayya zuwa wajen wani sansani da ke gefen garin.

Ƙasa ta biyu mafi yawan jama’a a Afirka da kusan mutane  miliyan 120, Habasha, ƙasa da kusan kabilu 80, ta shiga rikici wanda ya daidaita ƙasar da kuma haifar da yan gudun hijira da dama.

Leave a Reply