Sojoji sun lakaɗawa ma’aikatan wutar lantarki duka kan rashin ba da wuta

1
768

Sojoji ɗauke da makamai sun kai farmaki ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki na KAEDCO a jihar Kebbi tare da cin zarafin ma’aikatan da suka ka sa samar musu da wutar lantarki a barikinsu.

Manajan kamfanin na yankin jihar Kebbi, Gaddafi Ibrahim, ya tabbatar da faruwar harin a wani faifayin bidiyo da aka yaɗa ta yanar gizo, inda ya ce sojojin sun lakaɗawa ma’aikata da kwastomomi duka a ranar Asabar.

Ya ce sojojin sun zargi KAEDCO da rashin samar da isasshiyar wutar lantarki a barikin duk da sadaukarwar da suka yi wa ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Hukuma wutar lantarki ta nemi afuwar kwastomomin ta na Kano

Ya ce mutane 14 da suka haɗa da jami’an tsaro masu zaman kansu, kwastomomi, da ‘yan kasuwa an yi musu dukan tsiya ba tare da tausayi ba tare da tilasta musu yin tsalle-tsalle da gwale-gwale daga jami’an soji.

“Da misalin ƙarfe 1:00 na rana, jami’an soji suka mamaye ofishinmu. Ina zaune tare da babbana wanda ya zo daga Sokoto.

Da muka fito waje, sai muka ga suna cin zarafi ga wasu ma’aikatanmu da abokan cinikinmu. “An umarce su da su cire tufafinsu su yi tsallen kwaɗo.

“Lokacin da muka tuntuɓe su, sai suka ce mana sun zo ne domin yin ƙorafin cewa ba a ba su isasshen wutar lantarki ba. Sun kuma ce rashin mutunci ne a gare mu mu samu haske mu bar su cikin duhu.

“Na shaida musu cewa a cikin watanni shida da aka kawo a nan, ban taɓa samun koke daga barikin ba, amma sun sha alwashin ba za su bari masu yin tsallen kwaɗo su tsaya ba har sai an dawo da hasken a cikin bariki.

Sai na ba da umarnin a dawo da haskensu nan take,” inji shi. Gaddafi ya lura da cewa al’amarin zai yi ta zubar da jini da bai hana ‘yan sandan tafi da gidanka da ke ofishin shiga tsakani ba.

Ya ƙara da cewa “‘yan sandan wayar tafi da gidanka da ke ofishin sun so yin turjiya amma sai na hana su.” Wata sanarwa da mataimakin babban sakataren ƙungiyar manyan ma’aikatan wutan lantarki da kamfanonin haɗin gwiwa, SSAEC mai kula da Arewa, Haruna Tinau, ya fitar, ta yi Allah-wadai da harin da sojoji suka kai wa membobinsu tare da neman a dakatar da barikin Birnin Kebbi gaba ɗaya har sai an kawo masu laifin.

Tinau ya ce, “Harin ya zo mana ne a cikin rashin kunya, duk da cewa har yanzu ba mu farfaɗo ba daga tsare membobinmu a Fatakwal Electric bisa irin wannan dalili da hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta yi.

“Wannan ba abin yarda ba ne, kuma dole ne a bijire masa domin a hana wasu masu irin wannan mugun nufin ɗaukar irin wannan mummunan mataki nan gaba kaɗan.

“Ƙungiyar ta buƙaci a rufe barikin Birnin Kebbi gaba ɗaya har sai an gurfanar da masu laifin.

“Ƙungiyarmu ba za ta daina kallon wannan rashin hankali da wasu ƙungiyoyi ko ɗaiɗaikun mutane suke yi ba, don haka muna ƙira ga membobinmu na Birnin Kebbi da su nisanci ofisoshin ku har sai an tabbatar da tsaron ku.”

Ba a samu jin ta bakin sojojin Najeriya domin jin ta bakinsu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto

1 COMMENT

Leave a Reply