Daga Ibraheem El-Tafseer
Dakarun sojin Najeriya sun ceto wasu mutane tara da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.
Kazalika, dakarun rundunar Hadarin Daji sun kashe ‘yan fashin daji 10 a harin da ta kai a safiyar ranar Talata.
Wata sanarwa daga rundunar ta ce dakaru sun samu bayanan sirri ne na ‘yan bindigar da ke shirin sace wasu daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su daga jihar Sakkwato zuwa ƙauyen Gadazaima na jihar Zamfara.
Sojojin sun yi kwanton-ɓauna a cikin ƙauyen, inda aka yi musayar wuta tsakanin sojojin da ‘yan bindigar na tsawon sa’o’i.
“Ƴan bindiga 10 ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka tsere bayan an jikkata su,” a cewar sanarwar.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun wurare tace mai 36, sun kama mutane 22 a yankin Neja Delta
“Da yawan ‘yan bindigar sun nutse cikin wani kogi da ke kusa da ƙauyen a yayin da suke ƙoƙarin tserewa. An yi nasarar kama biyu da kuma makamai masu yawa, da ƙudi naira miliyan 2,410,000, da kuma keken ɗinki.”
[…] KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe ‘yan fashi 10 tare da ceto mutane tara a Zamfara […]
[…] KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe ‘yan fashi 10 tare da ceto mutane tara a Zamfara […]