Sojoji sun kashe ‘yan bindiga a Katsina, sun ƙuɓutar da mutane a Zamfara

0
130

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ‘yan bindiga 10 a jihar Katsina tare da ƙuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Ta bayyana haka ne ranar Alhamis a wata sanarwa da Kyaftin Ibrahim Yahaya, kakakin Rundunar Operation Hadarin Daji (OPHD ya fitar).

Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun sojin sun ƙuɓutar da mutum tara, mata biyar da ƙananan yara huɗu, da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Rundunar ta ce an ƙuɓutar da mutanen ne a garuruwan Ɗansadau da Ɗandalla da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Sojojin sun ce ‘yan ta’adda da dama sun tsere ɗauke da harbe-harben bindiga a jikinsu.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe mahara 14, sun ceto mutum 14

“Ranar 3 ga watan Janairun 2024, Rundunar OPHD ta ƙaddamar da hare-hare a maɓoyar ‘yan ta’adda a ƙananan hukumomin Batsari da Safana da ke Katsina, inda ta kashe ‘yan ta’adda 10 yayin da wasu suka tsere ɗauke da harbe-haren bindiga a jikinsu,” in ji sanarwar.

Rundunar ta ce ta ƙwace makamai da alburusai da babura da kuma wayoyin salula daga wurin ‘yan ta’addan.

Jihohin Katsina da Zamfara sun daɗe suna fama da matsalar masu garkuwa da mutane, wadanda ke zuwa gidaje da gonaki har ma da makarantu suna ɗauke mutane.

A lokuta da dama suna kashe su ko da an ba su kuɗin fansa.

Hukumomi sun sha alwashin kakkaɓe waɗannan ‘yan bindiga, sai dai mazauna yankunan sun ce akwai buƙatar ƙara ƙaimi wajen magance matsalar.

Leave a Reply