Sojoji sun kama ɗan ta’adda Baleri, uban gidan Bello Turji

0
52
Sojoji sun kama ɗan ta’adda Baleri, uban gidan Bello Turji
Ƴan ta'adda

Sojoji sun kama ɗan ta’adda Baleri, uban gidan Bello Turji

Sojojin haɗin gwiwa sun kama Beleri, ƙasurgumin ɗan bindigar Najeriya da ake nema ruwa a jallo.

Baleri uban gida ne ga ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, wanda ya addabi al’ummar yankunan Jihar Zamfara da hare-haren ta’addanci da kuma satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Baleri wanda shi ma ɗan Zamfara ne ya jima yana addabar al’ummar jihar da ma wasu yankunan Nijar, musamman jihar Maraɗi.

Shi ne na 40 a jerin ’yan ta’adda da hukumomin Najeriya ke nema ruwa a jallo, har ta yi alkawarin lada mai tsoka ga duk wanda ya taimaka aka kamo shi.

Sojojin na Nijar sun sanar cewa an kama Beleri ne a garin Rigar Kowa Gwani da ke yankin Gidan Rumji na jihar Maraɗi a ƙasarsu.

KU KUMA KARANTA: Jiragen yaƙin Najeriya sun yi luguden wuta a sansanonin ƴan ta’adda a Zamfara

Rundunar sojin Nijar ta ce dakarun Runduna ta Musamman mai suna Farautar Bushiya sun yi nasarar kama Beleri ne da misalin ƙarfe 1 a kan iyakar ƙasashen biyu, a jihohin Zamfaran Najeriya da kuma Maraɗin Jamhuriyar Nijar.

An kama shi ne a lokacin ya yake tsaka da  ganawa da yaransa a shirinsu na kai hari a Najeriya da Nijar.

Leave a Reply