Sojoji sun hallaka ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, sun ƙwato makamai da kuɗi Naira miliyan 13

0
213
Sojoji sun hallaka ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, sun ƙwato makamai da kuɗi Naira miliyan 13
Kuɗaɗe da makaman da aka kama shi da su

Sojoji sun hallaka ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, sun ƙwato makamai da kuɗi Naira miliyan 13

Daga Jameel Lawan Yakasai

Sojojin Operation SAFE HAVEN sun hallaka wani kasurgumin mai garkuwa da mutane tare da kwato makamai, harsasai da kuma kudin fansa yayin wani aikin bincike a hanyar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 9 ga Yuli, a kan hanyar Wamba–Jos, a Agameti, karamar hukumar Sanga ta jihar, a cikin ci gaba da gudanar da Operation LAFIYAN JAMA’A.

A cewar sanarwar da Manjo Samson Nantip Zhakom, jami’in hulda da jama’a na Operation SAFE HAVEN ya fitar, sojojin sun kafa wani binciken gaggawa a kan hanyar inda suka cafke motar Volkswagen mai lamba JJN 336 YZ dauke da mutane uku.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta yanke hukuncin rataye wani mutum mai laifin fashi da makami 

Ana zargin biyu daga cikin su sun tsere da gudu da suka ga sojojin, lamarin da ya sa jami’an suka dauki matakin gaggawa.

Binciken da aka yi ya nuna cewa motar na dauke da ramukan harsasai da tabon jini. Daya daga cikin wadanda aka tsinta a cikin motar ya yi yunkurin bai wa sojojin cin hanci da kudi amma aka kama shi bayan an ki amincewa da tayin.

Binciken da aka yi sosai a kan wanda ake zargin da kuma motar ya kai ga gano abubuwa kamar haka: bindigogi kirar AK-47 guda biyu, magazines guda biyu dauke da harsasai 30 na 7.62mm (na musamman), wayoyin hannu guda uku, wuka guda daya, kwallo guda daya, zoben asiri da dama, fitila guda daya, da kuma kudi naira miliyan 13,742,000 da ake zargin kudin fansa ne.

Leave a Reply