Daga Ibraheem El-Tafseer
Dakarun sojin Najeriya sun ce sun ceto mutum 40 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.
Dakarun da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji sun samu nasarar ceto mutanen ne a ƙaramar hukumar Bukkuyum na jihar.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa sojojin sun samu nasarar ce bayan samun bayanan sirri da ke cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba a ƙauyen Kyairu da Alkama da ke ƙaramar hukumar ta Bukkuyum.
Bayan nan ne sojojin suka tasamma garin da nufin kai samame domin ƙwato mutanen da ke hannun ‘yan bindigar a ranar Talata.
KU KUMA KARANTA: Ku ba mu dama mu kakkaɓe ‘yan ta’adda – sojojin Najeriya ga gwamnonin arewa
Sai dai sojojin sun yi bata-kashi da ‘yan bindigar na wasu sa’o’i kafin su fi ƙarfinsu da tilasta musu tserewa da kuma barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Mutanen da aka ceto ɗin da suka kai 40 tuni suka haɗu da iyalansu yayin da aka miƙa goma daga cikinsu kuma ga hannun Sarkin Gwashi domin haɗa su da iyalansu.
[…] KU KUMA KARANTA: Sojoji sun ce sun ceto mutum 40 daga hannun ‘yan bindiga a Zamfara […]
[…] KU KUMA KARANTA: Sojoji sun ce sun ceto mutum 40 daga hannun ‘yan bindiga a Zamfara […]