Sojoji sun ƙuɓutar da ɗaliban jami’a shida waɗanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Zamfara

3
288

An ƙuɓutar da ɗalibai shida daga cikin ɗalibai 24 na Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara waɗanda aka yi garkuwa da su da sanyin safiyar ranar Juma’a, kamar yadda jaridar News Point Nigeria ta ruwaito.

Wata majiya mai ƙarfi na soji na kusa da Kwamandan Birged 1 na Sojojin Najeriya Gusau, ta tabbatar wa da wakilinmu hakan, biyo bayan farmaƙin da ‘yan bindiga suka kai a yankin Sabon-Gida da ke ƙaramar hukumar Bunguɗu.

Ya ce a halin yanzu Kwamandan Birgediya Birgediya Janar Sani Ahmed ne ke jagorantar aikin tare da sauran jami’an tsaro a dajin da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar.

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama a farmaƙin da ake kai tare da ƙwato wasu makamai.

KU KUMA KARANTA: Bayan biyan miliyan biyar, ‘yan bindiga sun saki ɗaya daga cikin masu yiwa ƙasa hidima da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Tun da farko, wani ɗalibin makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya shaida wa ‘News Point Nigeria’  cewa an sace ‘yan makarantar sama da 24, galibinsu mata yayin harin.

Wani mazaunin unguwar Sabon-Gida mai suna Nazeer Sabon-Gida ya kuma tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar garin ne da misalin ƙarfe uku na safe inda suka fara harbe-harbe ba gaira ba dalili.

A cewarsa, an kai hari a ɗakunan kwanan ɗalibai uku, kuma ‘yan bindigar sun tafi da dukkan ɗaliban da ke cikin ɗakunan kwanan.

A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace ɗaliban.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar, a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Juma’a, ya ce har yanzu rundunar ba ta tabbatar da adadin ɗaliban da aka sace ba.

Ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin ceto.

3 COMMENTS

Leave a Reply