Sojoji da DSS sun daƙile yunkurin Boko Haram na kai hari a Kano

Wani ayarin sojojin ƙasa na Najeriya da jami’an hukumar tsaro ta DSS sun sami nasarar daƙile yunkurin wasu ’yan ta’adda na kai hari ƙaramar hukumar Gezawa da ke Jihar Kano.

Kakakin Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafin rundunar na X ranar Juma’a.

Ya ce sun kai samamen ne da nufin kama wasu da ake zargin ’yan Boko Haram ne da ke ƙoƙarin kai wani ƙazamin hari a Kano.

Ya ce, “A wani samame da muka kai maboyar ’yan ta’addan da sanyin safiyar Juma’a, 3 ga watan Nuwamban 2023, dakarun runduna ga 3 ta sojin ƙasa na Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an DSS, sun kai wani shiryayyen samame a ƙaramar hukumar Gezawa ta Jihar Kano.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Boko Haram sun kashe sama da mutane 40 a Yobe – ‘Yan sanda

“A sakamakon haka, dakarun sun sami nasarar kama waɗanda ake zargin ’yan Boko Haram ne su biyu, waɗanda yanzu haka suke hannunmu.

“A yayin samamen, dakarun sun kwato bindigogin AK-47 guda biyar, manyan bindigun AK-47 masu sarrafa kansu guda biyar, na’urar harbo jiragen sama guda daya, bama-bamai guda biyar, gurneti guda 10, kakin sojoji guda biyar sai jakunkunan saka bindigogi guda 10 da kuma wasu sinadaran haɗa bama-bamai.

“Haɗin gwiwa da aiki taren da ake samu tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaro da aka gani yayin wannan aikin ya nuna karara yadda dukkanmu muke kokarin haɗa kai don ganin bayan ta’addanci da ma duk wani ƙalubalen tsaro.

“Hakan kuma ya daɗa tabbatar fafutukar da sojojin Najeriya ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya,” in ji Kakakin sojojin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *