No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sojoji a Taraba sun kama masu garkuwa da mutane 10

Sojoji a Taraba sun kama gawurtattun masu garkuwa da mutane guda goma da suka addabi yankunan jihar da makwabta

Sojoji daga Birget na 6 da ke garin Jalingo a Jihar Taraba sun kama wasu mutane goma da ake zargin masu sace mutane ne.

Muƙaddashin kakakin rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya sanar da haka a ranar Talata.

Kyaftin Oni Olubodunde ya bayyana cewa daga ciki, sojoji sun yi nasarar kama wasu ’yan ta’adda takwas masu fashi da kuma sace mutane.

Ya ce waɗanda aka kama su ne suka hana jama’a sakat a kananan hukumomin Wukari da Donga da Ussa da Takum tare da wasu yankunan Jihar Biniwai.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kama ɗan ta’adda Baleri, uban gidan Bello Turji

“Binciken da sojoji suka gudanar ya nuna cewa dukkansu yaran wani kasurgumin ɗan ta’adda ne mai suna Terwase Akwaza wanda  ake masa lakabi da suna Gana” in ji Kyaftin Oni.

Ya bayyana cewa uban gidan waɗannan ’yan taaddan watau Gana, tuni aka kashe shi.

Kyaftin Oni ya kuma bayyana cewa an sami makamai tare da kayan sojoji da kudade a wajen ’yan ta’addan su takwas da sojojin suka kama.

Ya kuma bayyana cewa  sauran ’yan ta’addan biyu daga cikin mutanen. an kama su ne a kauyukan Galeri da Kwodo da suke Karamar Hukumar Ardo-Kola bayan sun Sami bayanan sirri.

Kyaftin Oni ya ce an sami bindiga kirar AK-47 tare da harsasai a hannun wadanda aka kama.

Ya ce waɗanda aka kama sun bayyana cewa su yaran wani kasurgumin dan ta’adda ne mai  suna Kadogo Fun, wanda ya fitini al’ummar yankunan Bangalala da  Kampani Zura da ke Jihar Filato.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...