No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sojoji 6 da ‘yan Boko Haram 34 sun mutu a wata arangama

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda 34 a wani artabu da suka yi da ‘yan Boko Haram a arewa maso gabashin jihar Borno sannan kuma sojoji shida sun mutu.

Rikicin ya faru ne a ƙauyen Sabon Gari lokacin da ‘yan ta’addan suka yi wa sojojin da ke komawa sansaninsu kwanton ɓauna, kamar yadda kakakin rundunar, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana a ranar Laraba.

Ya ce ‘yan ta’addan na ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne. Suna tafiya ne a kan babura da manyan motoci dauke da bindigogi lokacin da suka kai harin a ranar Asabar.

Dakarun tare da taimakon wasu dakaru na rundunar sa kai na Civilian Joint Taskforce da kungiyoyin ‘yan banga sun yi nasarar dakile harin, in ji shi.

Najeriya dai ta shafe shekaru 16 tana fama da tashe-tashen hankula a yankin arewa maso gabashin kasar da kungiyar Boko Haram ke haddasawa da kuma kungiyar ta ISWAP, wanda ya janyo asarar dimbin jama’a da na tattalin arziki da suka hada da gudun hijira da kuma matsalar jinƙai.

Buba ya ce sojoji 6 ne suka mutu a harin arangamar da wasu bama-bamai da aka dasa suka tashi suka raunata kwamandan ‘yan banga.

KU KUMA KARANTA: Sojojin saman Najeriya, sun shirya bukin ƙarshen shekara a Katsina

Hakazalika rundunar sojin saman Najeriya ta kai farmaki ta sama kan ‘yan ta’addan da suka tsere, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane 34 da aka kashe a rikicin, in ji Buba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...