Sojoji 23 ne suka mutu sakamakon harin da IS ta kai kan motar bas ɗin sojoji a Syria

Sojojin Syria 23 ne suka mutu yayin da wasu 10 suka samu raunuka da sanyin safiyar Juma’a, bayan da mayaƙan IS da ke da’awar kafa daular Islama suka yi wa wata motar bas ɗin kwanton ɓauna a lardin Deir al-Zour da ke gabashin ƙasar.

Mayaƙan IS sun kai hari kan motar bas a yankin hamadar birnin al-Mayadeen da ke gabashin garin Deir al-Zour, in ji wani mai sa ido kan yaƙi, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Syrian Observatory for Human Rights.

Ƙungiyar da ke sa ido a Birtaniya ta ce mayaƙan IS sun shirya kwanton ɓauna tare da buɗe wuta kan motar bas ɗin da muggan makamai.

KU KUMA KARANTA: Wani mutum ya sare kan ɗan shekara 84 a Ogun, shi ma ya mutu saboda ya ƙi yarda a kama shi

Sojojin Syria sun kasance cikin shiri a yankin hamada, inda suke neman sojojin da suka ɓace, yayin da maharan suka ɓace cikin hamada, kamar yadda hukumar sa ido ta bayyana.

Rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin sanarwar da ta fitar amma ba ta bayar da bayanai kan adadin waɗanda suka mutu ba.

A cewar cibiyar binciken, IS ta tsananta kai hare-hare a yankin hamada, inda ta ce mutane 387 galibi sojoji ne IS ta kashe a cikin sahara tun daga farkon shekara ta 2023.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *