Shugabannin ƙananan hukumomi sun maka Gwamnatin Kano a gaban ƙuliya

0
139

Shugabannin Ƙananan hukumomin Kano 44 sun Maka Gwamnatin Kano a gaban kotun tarayya, kan zargin yunkurin ɗibar kuɗinsu domin yin aikin wasu gadoji a birnin Kano.

Alfijir labarai ta rawaito sun maka gwamnatin ne da nufin a hana gwamnatin taɓa musu kuɗaɗensu na cikin asusun haɗaka da sukeyi da ita (Joint Account) sakamakon abinda sukace ana ƙoƙarin ɗibar kuɗin a aikin gadojin Ɗan Agundi da ta Tal’udu.

A Takardar Ƙarar me Lamba FHC/ABJ/CS/1733/2023, shugabannin sunyi Karar Gwamnatin Kano ne, da kwamishinan shari’a na jihar da kuma Akanta Janar na Kano

Takardar me ɗauke Da Kwanan Watan Jumu’a 29 Ga Watan Disamba, ta roki kotun ta hana Gwamnatin Kano tana musu kuɗin nasu domin yin aikin gadojin 2.

Leave a Reply